News: Jita jita Akan Bola Tinubu Na Daukan Mataimaki Musulmi

0
Karshen Jita jita akan Tinubu

Karshen Jita jita akan Tinubu

Jita jita Akan Bola Tinubu Na Daukan Mataimaki Musulmi…..

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yadawa na cewa yana da niyyar zabar dan uwansa musulmi a matsayin abokin takararsa. Wanda Jaridar “Leadershiphausa” ta rawaito.

Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida yayin taron gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar jiya a Ekiti gabanin zaben gwamnan jihar da ke tafe.

Ya nisanta kansa daga wannan jita-jita, yana mai jaddada cewa yin hakan bai dace da tsarin dimokuradiyya ba, kuma masu yada wannan jita-jitar suna yi ne don kawo masa cikas wajen lashe zaben dake tafe na 2023.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *